Kungiyar masu dakon mai, a ranar laraba ta yi barazanar janyewa daga masu lalatattun titunan Najeriya matukar Gwamnatin tarayya bata gyara su ba kafin saukar rwan daminar badi.

Shugaban kungiyar masu dakon man ta kasa, Salimon Oladiti ne ya bayyana hakan a Abuja a wata sanarwa da mai lura da sashin hulda da jama’a na kungiyar ya Abdulkadir Garba ya sanyawa hannu.

A cewarsa, wannan gargadi da suke yi yana zuwa ne a sakamakon muguwar lalacewar da hanyoyin motar suka yi, kuma yace wannan abu zai shafi dakon mai da rarraba shi a jihohin kasarnan.

“Duk da ziyarar da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osibanjo ya kai, sannan yabi hanyoyin da suke isa zuwa ga gadar Tabatu wadda take cikin mawuyacin hali, kuma itace hanyar da ta wuce har zuwa Jebba da Mokwa hanyar duk ta lalace matuka”

“A sabida haka, muke kira ga Gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa akan gyrana wadannan hanyoyi, sabida nan ba da jimawa ba damina zata sauka, kuma hanyoyin zasu kara lalacewa ta yadda binsu zai zama da bakar wahala”

“Hanyoyin da lalacewarsu ta bayyana, ya zama dole a gyara su cikin gaggawa,ko kuma direbobin tankar dakwonmai su kaurace musu”

“Wadannan hanyoyi sune suke sada kudu da Arewa ta Badun – Mosimi da Ejigbo da kuma babbar tashar mai dake Warri-Kalaba sannan da tashar mai dake Ilori-Ore, duk inda za’a yi zirga zirga da mai sai ani wadancan hanyoyi zuwa defo defo”

“Mun goyi bayan ayi amfani da defo defo da muke da su ba sai na Legas kadai ba, sabida rage cunkoson manyan motoci a Apapa dake jihar Legas, wannan kuma zai taimaka wajen maganin karancin man da ake samu”

NAN

LEAVE A REPLY