Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II

Hassan Y.A. Malik

Kungiyar masu ruwa da tsaki na ‘yan addinin Kirista na yankin arewa, NOSCEF, ta gargadi Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi da ya shiga taitayinsa kan irin furuce-furacensa da ka iya haifar da rashin zamna lafiya da tashin hankali a fadin Nijeriya.

Wannan batu na dauke ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi a garin Jalingo, jihar Taraba, mai dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar, Bishop Isaac Philip da David Ibi.

NOSCEF ta kalubalanci bayanin da Sarkin Kano ya yi a baya-bayan nan, inda ya zargi gwamnonin jihohin Taraba da na Binuwe, Darius Ishaku da Samuel Ortom, da horas da wasu mayaka na musammam da nufin kakkabe fulani makiyaya a jihohin biyu.

“Bamu manta da kalaman batanci da Sarkin Kano ya yi akan Gwamnanatin jihar Taraba ba, inda ya zargi gwamnatin da cewa ita ce ta kitsa kisan gillar da ka yi akan fulani da ya yi sanadiyyar mutane sama da 800 a shekarar da ta gabata.”

“Zargin na Sarkin Kano, ya yi shi ne da nufin assasa mummunar rashin jituwa tsakanin manoma mazauna jihar Taraba da kuma fulani makiyaya da ke shigowa jihohin biyu.”

“Wannan wani abin takaici ne matuka a ce, Sarkin, wanda daya ne daga cikin iyayen kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah, ya furta irin wadannan kalamai da za su iya tayar da gobarar rashin jituwa da haddasa gaba tsakanin al’ummatai,” a cewar sanarwar ta NOSCEF.

LEAVE A REPLY