Sheikh Bala Lau

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah JIBWIS ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau a ranar Litinin a jihar Jigawa ya bayyana cewar Gwamnatin jihar ta mallaka musu fili mai fadin hekta 65 domin samar da jami’ar Musulunci a Hadejia.

Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da ya kaddamar da bikin sayan Ragon Layya domin tallafawa marayu raunana da kuma talakawa marasa karfi sakamakon gabatowar sallar Eida-al-Adha.

A cewar JIBWIS, sun karbi takardar mallakar katafaren filin da zasu gina jami’ar wanda Gwamnatin jihar ta basu ta hannun Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Abubakar Maje.

Ya kara da cewar, tuni suka shirya tsaf domin kafa kwamitin da zai jagoranci ganin an samar da wannan jami’ah da kuma yadda zata fara aiki ba tare da wani daukan dogon lokaci ba.

Sheikh Bala Lau ya cigaba da cewarbisa la’akari da tarihin da jihar Jigawa take da shi na zaman lafiya, da kuma gudanar  da harkokin kasuwanci cikin kwanciyar hankali ya sanya suka zabi jihar a matsayin inda zasu kafa wannan jami’ah.

Haka kuma, Shgaban ya kara da cewar a shekara uku da suka gabata da kungiiyar ta tara fatun layya da suka karba daga hannun jama’a sun samu kimanin naira miliyan 264 a dukkan fadin Najeriya.

Yace anyi amfani da kudin ne wajen samar da gidan Talabijin na Manara da kuma gidan saukar baki na Sheikh Abubakar Gumi dake babban birnin tarayya Abuja tare kuma da samar da Masallaci da kuma dakin karbar Magani.

A nasa jawabin Shugaban kungiyar Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana cewar Gwamnatin jihar zata bayar da dukkan gudunmawar da ta dace domin ganin an samar da wannan jami’a cikin nasara.

LEAVE A REPLY