Hassan Y.A. Malik

Kugiyar Kiristoci da Fastoci ‘yan asalin Arewa, ACIPA, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi kokari su ceto kasar daga rashin kwarewar mulkin da Shugaba Muhamadu Buhari ke nunawa a bayyana a cikin mulkinsa.

ACIPA bata tsaya kan ‘yan Nijeriya kadai ba, kungiyar ta rubutawa kungiyar tarayyar kasasshe Afirka, kungiyar tarayyar Turai, kungiyar kasashe rainon Ingila, majalisar dinkin duniya da kuma kasar Amurka da su taimaka su amso kasar daga hannun matsa da ta ke sha a hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar ta ACIPA, Luke Shehu, ya fadawa manema labarai a wata ganawa da manema labarai a a garin Jos, cewa bukatar neman taimakon a karbo kasar daga hannun Shugaba Buhari ya zama wajibi ganin yadda ya ke gudanar da mulkinsa na kafa ‘yan uwa da abokai a madafun iko, inda hakan ya zama barazana ga musamman Kiristocin arewa.

A cewar kungiyar ta ACIPA, Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza wajen cimma hakkokinsa na farko da suka hada da tsare rayuka da dukiyar ‘yan kasa.

Shehu ya ci gaba da cewa “Duk da dai ba za mu zargi gwamnati kai tsaye da cewa ita ce ke daukar nauyin al’amaran ta’addanci a kasar nan ba, to, amma muna zargin gwamnati da jan kafa wajen fuskantar al’amuran ta’addanci a kasar nan.”

“Ya kamata gwamnati ta daina yaudarar ‘yan Nijeriya da cewa wai ta murkushe Boko Haram. Maganar gaskiya ita ce, bayan shekara 3 akan mulki, wannan gwamnati ta gaza murkushe Boko Haram duk kuwa da alkawarin da ta yi za ta ga bayan kungiyar cikin wata 6 da kama aiki.”

LEAVE A REPLY