Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau

Babbar kotun taarayya dake Kano, karkashin mai Shari’ah Zainab Abubakar, ta ki baiwa Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano iznin amfani da takardun tafiye tafiyensa domin tafiya aikin Umara a bana.

Kotun dai na tuhumar tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau kan batun kudin zabe da ake zargin ya karba naira miliyan 25, da kuma batun raba kudaden zabe Naira miliyan 950 da aka yi a gidansa.

Tun farko Malam Shekarau ya nemi kotun da tabashi fasfonsa domi yaje yayi ibadar Umara ta wannan shekarar, amma kotun taki amince masa, duk kuwa da cewar Malam Shekarau din ya bayyana kotun cewar zai tafi a ranar 30 ga watan Mayu ya dawo 28 ga watan Yuni.

Sai dai lauyan hukumar EFCC yayi tutsu akan wannan bukata ta Malam SHekarau, inda ya bayyana kotun cewar sam bai kamata mutumin da ake yiwa tuhuma irin wannan a bashi damar ficewa daga kasarnan ba, inda kotun ta yadda da batunsa ta kuma bayar da umarnin kada a  baiwa Shekarau fasfonsa.

 

LEAVE A REPLY