Firaministar Burtaniya, Theresa may tare da Shugaba Buhari a Landan

Firaministar Burtaniya, Theresa May, ta yi kira ga mahukuntan Najeriya da su baiwa ‘yan Luwadi damar auren junansu, daman sauran kasashe rainon Ingila.

Da take magana, a ranar Talata, a yayin wata tattaunawa da Shugabannin kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka a Westminster.

Tace bai kamata ace akwai wata doka da zata mayar da’yan Luwadi masu mugun zunubi ba, a yankin kasashen da ingila ta yiwa mulkin mallaka.

Uwargida Theresa May ta cigaba da cewa, mafiya yawancin dokokin da suke harata Luwadi ko auren ‘yan Luwadi a kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka, an kirkiresu ne daga Burtaniya, tace yanzu kuma Burtaniya ta dawo daga rakiyar wadannan dokokin da suka haramta ayyukan ‘yan Luwadi.

“A duk fadin duniya, dokokin da suka kuntatawa mutane an yisu ne shekaru masu tsawo, wanda suke cutar da rayuwar miliyoyin mutane a duniya”

“Takurawa ‘yan Luwadi da ake yi, da kuma kin baiwa mata cikakken ‘yancinsu bai dace ba”

“Ina sane da cewar a baya, wannan kasar (Burtaniya) ta taba yin dokokin haramta ayyukan Luwadi, na san cewar a wancan lokacin kuskure ne yin wannan doka, kamar yadda kuskure ne a yanzu ma ci gaba da irin wannan doka”

“A matsayina na Firaministar Burtaniya, Ina mai yin nadama da nuna damuwata kan wadancan dokokin da suka musgunawa ‘yan Luwadi a baya, a matsayinmu na dangi dole mu baiwa kowa ‘yancin abinda ya dace da shi”

“Babu wanda zai kuma matsawa ‘yan Luwai da nuna cewar abinda suke yi din bai dace ba, kuma, kasar Burtaniya a shirye take domin taimakawa duk kasar da zata gyara dokokinta domin baiwa ‘yan Luwadi damar auten junansu” A cewar Firaministar Burtaniya, Theresa May.

“As the UK’s prime minister, I deeply regret that those laws were introduce…as a family, we must respect one another’s cultures and traditions, but we must do so in a manner consistent with equality, as it is clearly stated in the Commonwealth charter.

“Nobody should face discrimination or persecution because of who they are or who they love and the UK stands ready to help any Commonwealth member wanting to reform outdated legislation that makes such discrimination possible,” she added.

LEAVE A REPLY