Muhuyi Magaji Rimin-Gado

Babbar kotun tarayya dake da mazauninta a Gezawa a ranar Litinin ta bayarda umarnin a damke mata Shugaban hukumar karbar koke koke da korafin jama’a ta jihar Kano Muhuyi Magaji Riminin-Gado.

Jaridar Daily Nigerian ta habarto cewar Muhuyi Magaji ya caccaki kotun ne akan yadda take yiwa yunkurin hukumarsa kafar ungulu na yaki da abinda ya shafi cin-hanci da karbar rashawa da kuma zambar kudade da ake yiwa tsohuwar Akawun jiihar kano, Aisha Bello.

Haka kuma, mai shariah na babbar kotun, Muhammad Yahaya, ya bayar da umarni a wata takarda mai lamba K/M235/2018 a ranar 5 ga watan Yuli inda ya baiwa mukaddashin sufeton ‘yan sanda na kasa mai lura da shiyya ta daya dake kano da ya kamo mata Muhuyi Magaji Rimin-Gado duk inda ya ganshi.

Kotun ta bayyana cewar Muhuyi yaki bayyana gaban kotun tun cikin ruwan sanyi da kotun ta yi kira a gareshi da ya gurfana a gabanta, a saboda haka kotun na zarginsa da rashin mutunta umarnin kotu da kuma yin katsalandan a harkokin Shari’ah.

LEAVE A REPLY