Olisa Metuh

Babbar kotun tarayya a birnin Abuja ta bayyana cewar zata cigaba da sauraren karar da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kai  tsohon kakakin jam’iyyar PDP na kasa Olisah Metuh akan zargin amundahana da kudaden zabe.

Mai shariah Akon Abang shi ne ya bayyana cewar kotun zata cigaba da yiwa Metuh shariah ko da bai bayyana a gaban kotun ba, ya fadi hakan ne a lokacin da lauyan da yake kare Metuh Emeka Etiaba SAN ya nemmi a dage cigaba da sauraren shariah kasancewar wanda yake karewa baya jin dadi.

LEAVE A REPLY