Babbar kotun dake Abalakalai ta yankewa wasu muggan ‘yan fashi da makami su shida hukuncin rataya.

Daya daga cikin mutanan Micheal Okwuome, kotun ta same shi da laifin aikata fashi da makami a ranar 12 ga watan Yuli na shekarar nan 2018, mai SHariah Elvis Ngene ne ya jagoranci zaman kotun.

Wani dan fashin kuma mai shekaru 39, an same shi ne da laifin yiwa wasu dalibai fashi a dakin kwanansu dake Lagacy Hostel a jami’ar jihar Ebonyi mai suna ‘Ebonyi Satate University’ a babban birnin jihar Abakalaki a ranar 26 ga watan Mayun 2017.

Haka kuma, an samu Emeka Ezra da laifin satar wayar Nokia 210 da agogon hannu da Na’urar kwamfuta kirar Hp da wayar Tecno G9 da wata jakar makaranta da katin cirar kudi na Diamond Bank.

Sannan kuma, ya yi wata mai suna Loveth Cresent fashin zunzurutun kudi Naira dubu dari da sha daya da kuma Naira dubu hudu.

Sauran ‘yan fashin suma an same su da laifin fashi da kuma kisan kai.

LEAVE A REPLY