Wata kotu a jihar Legas ta yankewa wani mutum mai shekaru 58 hukuncin daurin shekaru 60 a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin yi wa yarinya mai shekaru 6 fyade.

Gwamnatin jahar Legas ita ta gurfanar da mutumin mai suna Obinna Izegben a gaban kotu.

Alkalin kotun, Mai shari’a Sybil Nwaka, ya ce laifin ya saba da sashe na 137 na kundin dokar jahar Lagos, 2015.

Ya ce bangaren masu kara sun tabbatarwa kotun cewa Izegben ya aikata wannan laifi, a don haka ne kotun ta yanke masa wannan hukunci.

Banda zaman gidan yarin, Izegeben zai kuma fuskanci ayyuka masu tsauri a gidan yarin.

A yayin da ya ke nuna takaicin shi game da lamarin, alkalin ya ce zamani ya zo da yara ba su tsira ba a hannun malaman su, ‘yan uwan su har ma da iyayen su.

Ya yi kira ga yara da su yi gaggawar kai karar duk wanda ya ci zarafin su ta wannan hanya ga hukuma.

LEAVE A REPLY