Wata kotun lardi mai daraja ta 1 dake Kubwa a Abuja, a ranar Juma’a ta daure wani dalibi mai shekaru 27, Aonover Iowuese gidan maza inda zai shafe watanni hudu sabida kama shi da akai yana satar jarabawa.

Dalibin, Iorwuese wanda dan asalin garin Gboko ne na jihar Binuwai, kotu ta same shi da laifi bayan ya amsa laifinsa akan zarge zarge guda biyu da ake yi masa na satar jarabawa.

Dalibi ya roki kotu afuwa, inda yace kuskure ne aka samu, kuma ya dau alkawarin ba zai kuma ba.

Alkalin kotun, Mohammed Marafa, ya baiwa dalibin zabin biyan tarar naira 40,000 ko wata hudu gidan yari. Sannan ya gargadi dalibin da kada ya kuskura ya kara yin satar jarabawa.

Mai gabatar da kara, Babajide Olanipekun, tun faro ya shaidawa kotun cewar, wata mai suna Mary Abraham dake titin NEPA a unguwar Kubwa a Abuja, ita ce ta gabatar da korafi a caji ofishin ‘yan sanda a ranar 13 ga watan Janairun nan.

NAN

LEAVE A REPLY