Ibrahim El-Zakzaky

Babbar kotun tarayya dake da mazauni a jihar Kaduna ta sake dage Shariar da take yiwa Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa Zeenatu da kuma kungiyarsu ta IMN zuwa ranar biyu ga watan Agusta mai zuwa.

Mai Shariah na babbar kotun Gideon Kurada ya dage sauraren karar ne domin baiwa mutane byun da ake tuhumarsu tare da jagoran ‘yan Shiar damar bayyana a gaban kotun a zama na gaba.

Sai dai kuma lauyan da yake kare jagoran na ‘yan Shiah Maxwell Kyom ya bayyana cewar sauran mutum biyun da kotu tace tana jiran bayyanarsu har yanzu babu wanda ya sanar musu da cewar kotu na nemansu.

Sai dai lauyan bai bayyana sunayen mutanan biyu ba.

LEAVE A REPLY