Patience Jonathan

Daga Hassan Y.A. Malik

Alkali Nnamdi Dimgba na Kotun gwamnatin Tarayya da ke Abuja ya mallaka wa gwamnatin tarayya wasu kadarorin matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Patience Jonathan, na wucin gadi.

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ce dai ta mika wannan bukata ga kotun tare da bukatar a yi fatali da ikirarin Patience game da kadarorin.

Hukumar, ta bakin lauyanta, ta fada wa kotun cewa ta na kan gudanar da bincike game da rashin bin ka’ida wajen mallakar kadarorin.

A don haka kotun ta bai wa hukumar wa’adin kwanaki 45 domin ta kammala binciken na ta, tare da baiwa gwamnati mallakin kadarorin na tsahon wannan lokaci.

Haka kuma an baiwa hukumar damar kara neman karin kwanaki idan ta na bukatar haka wajen gudanar da binciken.

Kadarorin dai wasu maka-maka gidaje ne da ke babban birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY