Tsohon Gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye

Wata babbar kotun tarayya dake Gudu a brnin tarayya Abuja, ta daure tsohon Gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye daurin shekaru 14 a gidan kurkuku sakamakon samunsa da aka yi da almundahana da dukiyar Gwamnati da ta kai Naira biliyan 1.16 a lokacin da yake Gwamnan jihar.

Dariye wanda a yanzu haka Sanata ne mai wakiltar jihar Filato ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, kotu ta same shi da laifi bayan da ake tuhumarsa akan laifuka guda shida da suke da alaka da zambar kudaden da yayi a lokacin da yake Gwamnan jihar.

LEAVE A REPLY