Daga Hassan Y.A. Malik

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ebuta Meta, jihar Legas, a ranar juma’ar da ta gabata ta tasa keyar wani mutum dan shekaru 42 da haihuwa da aka bayyana sunansa da Eze Onijekachi zuwa gidan kaso bisa zarginsa da kawar da budurcin kanwar matarsa wacce ke zama a gidansa tana rainon jaririnsa shi da mai dakinsa kuma yaya ga yarinyar da lalata.

Kodayake dai wanda ake zargin, Onijekachi, da ke zaune a gida mai lamba 44 da ke kan titin Joseph Babatunde, a unguwar Ajangbadi, jihar Legas ya ki amsa laifin da a ke zarginsa da shi na yin lalata da ƙanwar matarsa, amma shi mai shigar da ƙara, Sufeta Onime Idowu ya shaidawa kotu cewa wanda a ke zargi ya aikta laifin ne a ranar 16 ga watan nan da muke ciki na Mayu da misalin karfe 2:00 na dare a gidansa da ke adireshin da ke a sama.

Sufeta Idowu ya fadawa kotu cewa laifin dai ya sabawa sashen doka ta 137 na manyan laifuka na jihar Legas da aka fitar a shekara ta 2015.

Mai shari’a Madam A.O. Adegbite, a yayin da ta ke gabatar da hukunci ta umarci kotu da ta ci gaba da tsare wanda a ke zargi tare kuma da mika karar zuwa kotun laifuka na musamman da ke Ikeja, babban birnin jihar.

Mai shari’a Adegbite ta daga sauraren karar a waccan kotu zuwa ranar 25 ga watan Yuni, 2018.

LEAVE A REPLY