Charles Okah

Daga Hassan Y.A. Malik

Mutumin da ya tashi bom din ranar bikin samun ‘yancin Najeriya a Abuja da aka dana  a shekarar 2010, Charles Okah zai yi zaman gidan yari na rai da rai.

Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Laraba ta yankewa Okah wannan hukunci shi da Obi Nwabueze wanda suka aikata wannan danyen aiki tare.

Henry Okah, wanda dan uwa ne ga Charles Okah ya taba fuskantar irin wannan hukunci bisa laifi iri wannan (na tashin bom) a kasar Afirka ta kudu a lokacin yana zama a can.

In ba a manta ba dai, mutae da dama ne suka rasa rayukansu a wancan hari na ranar 1 ga watan Oktoban 2010, a lokacin Goodluck Jonathan na mulkin kasa.

Alkalin da ya zauna akan karar, Mai shari’a Gabriel Kolawole, a wata doguwar shari’a da ta shafe awanni hudu da rabi ana yi, ya bayyana cewa kotu ta samu wanda ake kara da shirya tare da tashin bom a ranar 15 ga watan Maris, 2010 a Warri, inda haka ya yi sanadiyyar rasa ran mutum guda, da kuma shirya tare da tashin wani bom din a ranar 1 ga watan Oktoba, 2010 a kusa da Eagle Square a Abuja, wanda haka ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

 Abokin a cikin laifin Okah, Obi Nwabueze, kotu ta gano cewa ya kasance yaron aike ga Okah, haka kuma shi ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 1.2 da aka yi amfani da su wajen sayen motocin da aka kai hari da su a Warri, inda shi kuma Okah ya samar da Naira miliyan 2 da aka sayi motoci 4 da aka kai harin Abuja da su.

LEAVE A REPLY