Jphn Kayode Fayemi

Wata kotu a babban birnin tarayya aAbuja ta sharewa tsohon Ministan ma’adanai kuma dan takarar gwamnan Ekiti Kayode Fayemi hanyar tsayawatakara, inda ta cire masa takunkumin da Gwamnatin jihar ta sanya masa na farar takarda da ake kira ‘White Paper’ a Turance.

A halin yanzu dai kotu ta bayyana cewar Fayemi na iya rike dukkan wani mukami na siyasa bugu da kari kuma zai iya tsayawa takara a dukkan matakai idan yana son hakan.

Mai Shari’ah Othman Musa yayi fatali da karar da jam’iyyar APP ta kai Fayemi inda take kalubalantar tsayawarsa takarar Gwamna, a cewarta yana da takunkumin nan na farar takarda da ta hana shi tsayawa ko wanne irin mukami na siyasa.

 

LEAVE A REPLY