Daga Hassan Y.A. Malik

Wani barawo da ya saci buhuhunan kwakwa guda 16 ya gurfana a gaban kotun da ke Badagry a jahar Lagos, a yau Talata.

Barawon mai suna Demola Fadipe ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Mayu a kasuwar kwakwa da ke yankin Agabalata a Badagry, kamar dai yadda dan sanda mai kara, Akpan Ikem ya shaidawa kotun.

”An aiki Demola da wadannan buhunan kwakwa domin ya kai wa wani kwastoma, sai ya zarce da su gidan sa ya fara rabawa mutane da makwabta kyauta.”

”Mun damke Demola a lokacin da ya ke watanda da wannan kwakwa a unguwar su.”

Sai dai Demola ya musanta aikata wannan laifi.

Alkalin Kotun, Jimoh Adefioye ya bada belin shi akan Naira 200,000 tare da mutane 2 da za su tsaya masa.

Za a ci gaba da sauraron karan ranar 18 ga watan Yuni.

LEAVE A REPLY