Olisa Metuh

Babban kotun tarayya dake Abuja, ta nuna shakkunta game da gaskiyar halin da Olisa Metuh yake ciki na rashin lafiya, kotun na da shakkun anya kuwa tsohon kakakin jam’iyyar PDP na kasa ba shi da lafiya da gaske, ko kuma rufar kura ne kawai da fatar akuya,

Mai Shariah Okon Abang ya bayyana a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da hukunci kan batun baiwa Metuh fasfonsa domin zuwa kasashen waje don duba lafiyarsa, alkalin ya nuna shakku kan batun rashin lafiyar Olia Metuh.

A cewar alkalin kotun, “Ina cike da shakku game da wannan rashin lafiya da ake cewar Olisa Metuh yana fama da ita, me yasa tun a baya bai nemi a bashi fasfo dinsa ba sai yanzu? Gaskiya ina cike da shakku kan wannan batun rashin lafiya”

 

LEAVE A REPLY