Daga Hassan Y.A. Malik

Wata kotun majistare da ke Kano a yau Laraba ta tasa keyar wasu maza 3 zuwa gidan kaso sakamakon zarginsu da yi wa wata mace mai shekaru 30 da haihuwa fyade.

Wadanda ake zargin: Marcus Sani mai shekaru 30, Iliya Garba mai shekaru 40 da Halilu Musa mai shekaru 35 da ke zaune a Fammar cikin karamar hukumar Kibiya, jihar Kano na fuskantar zargin guda 3 da suka hada da: hadin gwiwa wajen aikata laifi, taimakekeniya wajen aikata laifi da kuma fyade.

Alkalin kotun, Mai shari’a Muhammad Jibril ya umarci da a garkame wadanda a ke zargin har zuwa ranar 25 ga watan Afrilu inda kotu za ta ci gaba da sauraren karar a wannan rana.

Mai shigar da karar, Insifeto Pogu Lale ya bayyanawa kotu cewa wani mai suna Yusuf Musa ne da ke zaune a kauyen Fassi ne ya shigar da karar aikata fyaden ga ofishin ‘yan sanda na yankin Kibiya a ranar 11 ga watan Maris.

Lale ya ci gaba da cewa, a ranar 8 ga watan Maris ne dai da misalin karfe 1:30 na rana wadanda a ke zargin suka farma matar mai shekaru 30 a kan hanyarta ta dawowa daga aike, inda suka yi lalalta da ita ta karfin tsiya, kuma a yanzu haka aika-aikan da suka yi, matar ta samu shigar juna biyu.

Wadanda a ke zargin sun musanta zargin da a ke yi musu.

Insifeto Lale ya bayyana cewa wadannan laifuka sun sabawa kundin hukunta laifuka na Penal Code sashe na 97 da na 83 da na 283.

LEAVE A REPLY