Daga Hassan Y.A Malik

Kotu a jihar Sokoto ta tasa keyar wata ‘yar kasuwa mai shekaru 30 da haihuwa da aka bayyana sunanta da Rabi’ah Mustapha zuwa gidan kaso bayan da aka sameta da laifin kashe dan gaba da Fatiha da ta haifa.

Rabi’ah, da ke zauna a unguwar Asada cikin jihar Sokoto ta gurfana a gaban kotu ne bisa laifuka biyu, da suka hada da: Aikata mummunan laifi da kuma kare rayuwar dan karamin yaro da bai ji ba bai gani ba.

Rabi’ah ta amsa laifin da a ke zarginta da shi, inda nan take mai Shari’a Abubakar Adamu ya bayyana cewa duk da cewa kotun ba ta da ‘yancin yanke hunkunci laifin da a ke zargin Rabi’ah da shi, ya umarci da a tasa keyarta zuwa gidan maza..

Mai Shari’a Abubakar Adamu ya daga sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Afrilu, tare kuma da daukaka shari’ar zuwa kotun da ke ikon sauraron karar.

Kafin wannan hukunci dai sai da mai gabatar da kara, Kyaftin Umar Rabi’u, ya shaidawa kotu cewa, wacce a ke zargi ta aikata laifin ne a ranar 3 ga watan nan na Maris da mu ke ciki, a unguwar Asada, jihar Sokoto.

Ya ci gaba da cewa, Rabi’ah ta haifi yaro namiji ba tare da aure ba, kuma ta yanke hukunci kashe yaron ta hanyar makura, sannan ta jefa gawar a cikin shadda.

Ya ce wannan laifi ya sabawa sashen doka na 235 na kundin Penal Code.

LEAVE A REPLY