Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar litinin ya bayyana goyon bayansa ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai kan kudurinsa na korar Malaman Firamare 22,000 daga aiki.

Gwamnan jihar Kaduniya ya bayyana aniyarsa ta korar Malaman Firamare 22,000 wadan da suka kasa cin jarabawar gwaji da aka yi musu.

Tuni dai kungiyoyin kwadago da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani suka yi Allah-wadai da wannan yunkuri na Gwamna el-Rufai na korar Malaman da suka kasa cin jarabawar gwajin da aka yi musu.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a Abuja, wajen wani taron karawa juna sani da Majalisar zartarwa take gudanarwa a Abuja.

LEAVE A REPLY