Sule Lamido, mai neman jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takarar Shugaban kasa

A ranar litinin dinnan da ta gabata ne, tsohon Gwamnanjihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Najeriya a 2019 idan jam’iyyarsa ta PDP ta sahale masa.

A cikin wasikar da ya rubuta zuwa ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a ranar 22 ga wannan watan, Sule Lamido ya bayyana wasu daga cikin dalilinsa na fitowa wannan takara, da kuma abubuwan da yake son mayar da hankali akai idan ‘yan jam’iyyar ta PDP sun zabe shi a matsayin dan takararsu a zaben da ke tafe.

Ya bayyana a cikin wasikar tasa mai shafi uku, cewa,shugabannin Najeriya da suka gabata, sun dora kasar a kan turba ta hadin kai da tabbatar da kasa daya al’umma daya. Yace matukar ana son cigaba dole a yi batun kasa daya dunkulalliya.

Batun yankuna ko Kudu da Arewa ba zai kaimu gaci ba, dole mu yarda mu duka ‘yan najeriya ne, Musulmi da Kirista mu sadaukar da kawukanmu domin gina wannan kasa tamu, a cewar Sule lamido.

Sule Lamido dai kusan shi ne mutum na farko da ya fara bayyana aniyarsa a hukumance ta tsayawa takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, duk kuwa da ana ganin cewar, ‘yan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar suna da yawa.

Daga cikin wadan da ake ganin zasu nemi jam’iyyar ta tsayar da su takarar Shugaban kasa sun hada da tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau wanda ya shiga PDP a 2014, da kuma tsohon Ministan ayyuka na Musamman Kabiru Tanimu Turaki SAN, wanda ake ganin makusanci ne na kud-da-kud da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose wanda shima ya nuna aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa.

Bayan haka, ana ganin akwai wasu jiga jigan mutane da har yanzu suna cikin jam’iyya mai mulki ta APC wadda ake ganin suma zasu tsallako jam’iyyar ta PDP domin yin takarar Shugaban kasa.

Sai dai abin tambayar anan shi ne, ko PDP zata iya tsayar da Sule Lamido a matsayin dan takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa? Idan aka yi la’akari da kwarewa da gogewar siyasa irin ta Sule Lamido da kuma yadda ya tsaya kai da fatawajen ganin jam’iyyar ta PDP ta samu nasara a baya ma iya cewar, ba lallai bane PDP ta juyawa Sule Lamido baya.

Ganin cewar Sule Lamido na daya daga cikin mutanan da aka kafa PDP da su tun 1998, kuma tun wannan lokacin bai taba barin jam’iyyar ya tsallaka zuwa wata ba. Saura da me, za dai mu jira mu gama ganin sauran ‘yan takarar PDP su gama fitowa, sannan muga wa jam’iyyar zata sanya a gaba domin yi mata takarar Shugaba kasa a zaben 2019 dake tafe.

LEAVE A REPLY