Sule Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a ranar Litinin a birnin Abeokuta ya bayyana cewar yana da yakinin cewar jam’iyyar adawa ta PDP zata dawo kan karagar mulki a babban zaben 2019.

Sule Lamido wanda yake zantawa da manema labarai bayan gama ganawa da jagororin jam’iyyar PDP a jihar Ogun, inda ya shaida musu cewar jam’iyyar tayi dukkan shirin da ya dace domin dawowa kan karagarmulki a zabe mai zuwa.

 

Sannan kuma, ya bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar sun mallaki katin zabe domin jefa kuri’arsu ga jam’iyyar PDP tare da tabbatar da cewarjam’iyyar ta lashe dukkan zabubbuka domin dawowa da karfinta kan karagar mulki.

Da ya koma kan batun sa-toka-sa-katsen da ake yi tsakanin ‘yan majalisun tarayya da bangaren zartarwa, Sule Lamido yayi kira a dukkan bangarorin biyu da su bi tanade tanaden tsarin mulki a dukkan abubuwan da suka shafi cigaban kasarnan.

 

LEAVE A REPLY