Hassan Y.A. Malik
Wani saurayi mai tsananin kishi ya ya gididdiba budurwarsa da adda ya kuma barta kwance male-male cikin jini wai kawai don ya sameta tana hira cikin nishadi da wani saurayin, inda yanayin da ya same su ke alamta suna cikin soyayya ne.
Wannan lamari ya faru ne a cikin wata jiha cikin yankin gabashin Nijeriya da wanda ya daura labarin a shafinsa na facebook bai a bayyana sunan jihar ba.
Lamarin ya samu dogon sharhi daga mutane, inda suka yi ta Allah wadarai da wannan hali na rashin imani irin na wannan saurayi.
Wanda ya sanya labarin ya bayyana cewa tuni dai ‘yan sanda suka cafke saurin kuma suna kan yin bincike kafin su ingiza keyarsa zuwa gaban kuliya.

LEAVE A REPLY