Marigayi Khalifa Isyaku Rabiu

Daya daga cikin fitattun mutane a kano, mashahurin dan kasuwa a shekarun 1970 zuwq 1980, Khalifa Isyaku Rabiu ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.

Khalifa Isyaku Rabiu shi ne jagoran ‘yan darikar Tijjaniyyah na Najeriya.

Iyalan marigayi Sheikh Isyaku Rabiu sun tabbatarwa da DAILY NIGERIAN cewar, Malamin ya rasu a wani asibiti a birnin Landan na kasar Burtaniya a ranar Talata.

Ya rasu yabar matansa da ‘ya ‘ya da jikoki masu yawa, daga cikinsu akwai Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdussamad Rabiu.

LEAVE A REPLY