Sabon zababben Gwamnan jihar EKiti Kaypde John Fayemi ya karbi takardar shaidar samun nasarar zale zaben Gwamnan jihar Ekiti da aka kammala a ranar Asabar da ta gabata.

An dai gudanar da zaben ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin da Fayemi na jam’iyyar APC yayi nasara da karamin rinjaye.

Yayin da mataimakin Gwamnan jihar mai ci kuma dan takarar jam’iyyar PDP Olusola Kolafo-Eleka yazo na biyu da ratar da bata fi kuri’a dubu ashin ba.

Jam’iyyar PDP ta kasa dai ta yi watsi da sakamakon zaben na Gwamnan Ekiti inda ta bayyana cewar an tafka kazamin magudin da ya shallake hankali.

haka nan kuma, suma gamayyar kungiyoyin masu sanya ido a zaben sun bayyana cewar an yi kazamar cuwa cuwa a wajen fitar da sakamakon zaben Gwamnan na Ekiti, inda suka bayyana ranar Larabar nan a matsayin ranarda zasu fadi matsayarsu kan zaben na Ekiti.

LEAVE A REPLY