Mai taimakawa Shugaban kasa na musamman Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya shigar da koke gaban rundunar ‘Yan sanda ta jihar Kano kan ahinda ya kira kokarin dawo da siyasar banga da sara suka a yankin Kano ya kudu.

Kawu Sumaila ya yiwa kwamashinan ‘Yan sanda na jihar Kano korafin daurewa ayyukan saba gindi da Sanata Kabiru Gaya yake yi a yankin Kano ta kudu.

Sanata Kabiru Gaya da Hon. Kawu Sumaila na neman a tsayar da su takarar Sanatan Kano ta kudu a karkashin tutar jam’iyyar APC a jihar Kano.

Ana samun zazzafar adawa tsakanin magoya bayan bangarorin biyu a kafafen yada labarai musamman na Radiyo a jihar Kano.

Binciken Daily Nigerian Hausa ya gano cewar  kujerar Sanatan Kano ta kudu tana daga cikin kujerar da za yi gumurzu akanta a zaben fidda gwani na jam’iyyar AapC a jihar Kano.

LEAVE A REPLY