Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewar zata dauki malaman makaranta kimanin 1,900 dominkoyarwa a makarantun Firamare da Sakandire domin bunkasa harkar ilimi a jihar.

Kwamishinan ilimin jihar, Badamasi Chiranchi ne ya bayyana haka a tattaunawar da yayi da manema labarai a ranar Alhamis.

Badamasi yace, dominbaiwa sashen ilimi muhimmanci, Gwamnatin jihar Katsina ta ware kashi 35 na kasafin kudin 2018 a harkar ilimi.

“Gwamnatin jihar Katsina ta gyara makarantun Firamare 150 tare da na Sakandire 15 a shekarar 2017 da ta gabata”

“Haka kuma, Gwamnatin ta gina sabbin azujuwa a wasu makarantun kwana dake jihar, a dukkan mazabun sanata guda uku” Inji Kwamishinan ilimi.

Ya kara da cewar, Gwamnati tayi karin girma ga Malamai 1,000 na Firamare da Sakandire.

Yace, Gwamnatin Katsina ta ware miliyan 77 domin biyan iayaye kudaden da suka biyawa yaransu na jarabawar WEAC da NECO a shekarar 2017 da ta gabata.

A sabida haka,Kwamishinan ya bukaci iyayen da yaransu suka samu nasara a darasi biyar da su gabatar da takardunsu domin dawo musu da kudin da suka kashe na jarabawar.

LEAVE A REPLY