Gwamnan jihar Taraba DD Ishaku

A ranar litinin, ‘yan sanda a jihar Taraba, sun tabbatar da kisan mutum 3 a yayin da akalla mutum 6 suka jikkata a wani sabon rikici da ya auku a wani hari da aka kai kauyen Maisamari dake yankin karamar hukumar Sardauna.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar David Misal ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN wannan sabon rikici a birnin Jalingo, inda yace abin ya auku ne sakamakon wani bikin al’adun gargajiya da ake yi a yankin wanda ake kira Nding-chin.

Ance wannan biki dai shi ne irinsa na farko a yankin da lamarin ya auku.

Mista Misal yace, tuni aka dawo da doka da oda a yankin da lamarin ya auku, rundunar ta tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da da’a.

Godwin Silo, Mai rikon mukamin karamar hukumar Sardauna a jihar,ya shaidawa NAN cewar, Gwamnatin karamar hukumar ta haramta duk wani bikin al’adun gargajiya a yankin tun da jimawa, sabida yadda yake tayar da hatsaniya a baya.

Mista Sol, ya kara da cewar, mun cika da mamaki lokacin da muka ji ance wasu mutane sun shirya raye raye da kide kide a yankin da sunan bikin al’adun gargajiya wanda suna da masaniyar an hana.

Yace tun farko an tura jami’an tsaro yankin domin su tarwatsa mutanen da ke bikin, amma sabida yawan dumbin jama’ar da suke wajen, sai wajen ya hautsine.

Yace daga baya mutanan suka canja waje, inda suka je cikin dare suna yin rawa a wani guri daban, wani mutum da ake kira Yaya Ahamadun shi ne jagoran rawar.

“A lokacin da suke tsaka da cashiya ne, wasu mutane da ba’a san ko su waye ba suka farwa mutanen wajen, inda aka kashe mutum 3 tare da jikkata wasu”

Sai dai tuni hukumomi suka cafke wadan da suka shirya wannan biki wanda a halin yanzu suke tsare hannu jami’an tsaro.

NAN

LEAVE A REPLY