Shugaban karamar hukumar Kwande, Terdoo Kenti ya tabbatar da kisan mutane 7 tare da jikkata wasu 6 a yankin karamar hukumar tasa.

Kenti ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya ta wayar tarho cewar maharan sun kashe mutanan tare da yin garkuwa da wata mata a kauyen Tseadough dake yankin karamar hukumar.

Ya kuma shaidawa NAN cewar bayan kashe mutanan tare da jikkata wasu da aka yi a yankin, maharan sun kuma bankawa gidaje da dama wuta a yankin, inda nan ne garin Tibi na asali a jihar Binuwai.

Tuni aka ajiye gawarwakin mutanan da suka mutu a mutuware dake yankin, yayin da aka garzaya da wadan da suka ji raunuka zuwa asibiti.

Bayan haka kuma, Shugaban karamar hukumar yayi kira ga mutanan yankin da su kwantar da hankalinsu kuma su zauna lafiya, su jira hukumomin.

 

 

LEAVE A REPLY