Ministan ayyukan gona da raya karkara, Audu Ogbeh, ya bayyana cewar kasar Thailand ta zargi Shugaban Najeriya da karya musu tattalin arzikin Shinkafa, duba da yadda ‘yan Najeriya kwat kwata suka dena zuwa kasar yin odar shinkafa.

Ministan ya bayyana haka ne a wani taron kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan samar da takin zamani. Taron wanda ya gudana a fadar Shugaban kasa dake Aso Villa dake Abuja, a ranar juma’ar na.

Taron wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa ya jagoranta.

Mista Ogbeh ya bayyana cewar Jakadan kasar Thailand a Najeriya shi ne ya bayyana wannan batuu a lokacin da ya ziyarci ministan a watan Fabrairun da ya gabata.

A cewar ministan hakan wani abin alhafari ne ga Najeriya kasancewar ta bunkasa harkar noma ta yadda har ‘yan Najeriya na iya noma shinkafar da ake bukata a kasar.

 

 

LEAVE A REPLY