Kwamandan Hisah na jihar Kano, Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta samu korafe korafe har guda 106 a watan Maris kadai da suka hadarda Karuwanci, da sabanin da ake samu tsakanin miji da mata da kuma sabanin tsakanin makwabta, a cewar wani jami’in hukumar Umar Yahaya.

Malam Umar wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya shaidawa manema labarai a birnin Kano cewar, da yawan korafe korafen suna da alaka da shayarwa da bashi da kuma uwa uba shaye shayen kayan maye.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ya kara da cewar, yana daga cikin aikin hukumar kokarin ganin an yi hani da aikata munanan ayyuka da kuma yin umarni da aikata kyawawa.

Haka kuma, ya bayyana cewar, hukumar ta karbi kudin da ya kai Naira miliyan 5 daga iyaye maza domin baiwa matansu kudaden shayarwa ga yaransu.

Daga karshe Malam Umar ya bukaci al’umma da su taimakawa yunkurin hukumar Hisbah na ganin an tsarkake wannan al’umma daga miyagun ayyuka.

 

NAN

LEAVE A REPLY