Atiku Abubakar

Daga Hassan Y.A. Malik

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa matsalar da ke addabar Nijeriya ba ta da wata dangantaka da banbamce-banbamcen addini ko kabilanci

Atikun ya bayyana hakan ne a sanarwar da ya fitar don yi wa al’ummar Nijeriya barka da shagugulan bikin Ista (Easter), mai dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai.

A sanarwar, Atiku ya ja hankalin shuagabanni da su zama masu sadaukar da kawunansu wajen ganin an samu waraka daga dimbin matsalolin da kasar ke ciki a halin yanazu.

Wazirin Adamawan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi son juna da kuma sadaukarwa, abin ya ce na daga cikin wasu kyawawan halayen Yesu Almasihu.

“Ya zama wajibi ga shugabanni a kowane mataki da su yi koyi da kyawawan akidun Yesu Almasihu da suka hada da soyayya ga juna, sadaukarwa da kuma sadaka. Babu shakka wannan shi ne zai kawo karshen wannan abun da ya rabamu.”

“Kar mu bawa wadanda suke son su raba kawunanmu dama ta hanyar nuna musu cewa matsalarmu ita ce kabilar da ba tamu ba,” Atiku Abubakar ya ce.

LEAVE A REPLY