Dan takarar Gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Malam Salihu Sagir Takai ya kai ziyarar nuna goyon baya ya Shugabancin jam’iyyar PDP karkashin Rabiu Sulaiman Bichi a ranar Litinin.

A makon da ya gabata ne Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa tsohuwar jam’iyarsa ta APC.

A baya dai tare ake harkokin Siyasa tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Malam Salihu Sagir Takai, Sai dai a yanzu an raba gari.

Domin Malam Salihu Sagir Takai Yaki bin Malam Shekarau zuwa jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY