Kwamandan Hisah Aminu Daurawa

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta bayyana cewar ta kaddamar da wani gagaruminbincike kan wani sautin muryar wasu mata ‘yan madigo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta na zamani, inda aka jiyo ‘yan madigon na jifan juna da miyagun kalamai akan junansu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewar, a cikin faifan sautin muryar, an jiyo ‘yan madigon na sa’insa da juna inda kowacce ke jifan ‘yar uwarta da kalamai na abinda ya faru da ita na madigo.

An habarto cewar wannan sautin muryar ya yadu sosai a jihar Kano, abinda ya janyo hankalin jami’an tsaro inda suka mayar da hankali domin bincikar lamarin tare da gano su waye suke wadannan miyagun kalamai da suka shafi madigo a ciki.

Wakilin DAILY NIGERIAN  ya ruwaito mana cewar, ana kyautata zaton ‘yan matan da suke kalaman batsa da suka shafi madigo a cikin faifan sautin da aka nada, alamu sun nuna cewar ‘ya ‘yan wasu manyan mutane ne a jihar Kano.

Sai dai kuma, mataimakin kwamandan Hisbah na jihar mai lura da sashin bincike na musamman Idris Ibn Umar ya tabbatarwa da DALY NIGERIAN cewar tun kusan mako guda da ya wuce hukumar ta samu wannan faifan murya da aka nada, kuma tun likacin aka kaddamar da bincike akansa.

Ibn Umar ya kara da cewar binciken da sashin da yake jagoranta yake yi tare da hadin guiwar wasu sassan jami’an tsaro yana haifar da da mai ido, domin kuwa suna samun gamsassun bayanai dangane da lamarin.

 

LEAVE A REPLY