Mataimakin Gwamnan Kano Hafizu Abubakar

Tsohon mataimakin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya yanki fom din takarar Gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP Domin nuna bijirewa zabin da Kwankwaso yayi na ayyana surikinsa a matsayin dan takarar Kwankwasiyya.

Yanzu dai ana Iya cewar Kwankwasiyya ta rabu gida biyu. Kwankwasiyya Amana da kuma Kwankwasiyya Surikiyya. Idan ba a manta ba a karshen makon da ya wuce ne dai, Kwankwaso ya bukaci Hafizu Abubakar da Salihu Sagir Takai su koma su yi takarar Sanatan yankunansu na Kano ta kudu da Kano ta Tsakiya.

Sai dai duka  Malam Salihu Sagir Takai da Hafizu Abubakar sun bijirewa wannan umarnin na Kwankwaso, inda suka ki amincewa da yin takarar Sanata.

Bayan da Takai da Hafizu suka ki amincewa da bukatar yin takarar Sanata ne, Kwankwaso ya fito da Abba Kabiru Yusuf surikinsa domin yayi takarar Gwamna daga bangaren ‘Yan Kwankwasiyya.

Yanzu dai ana Iya cewar ‘Yan takarar Gwamnan Kano a PDP sun kai 6. Malam Salihu Sagir Takai da Ibrahim Ali Amin Little da Sadiq Aminu Wali da Jafar Sani Bello da Abba Kabiru Yusuf sai kuma Farfesa Hafizu Abubakar da ya shigo a yanzu.

LEAVE A REPLY