Malam Salihu Sagir Takai

Dan takarar Gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2015 da ya gabata ajihar Kano, Malam Salihu Sagir Takai,  ya kaddamar da kwamitin mutum 15 da zasu jagoranci yakin neman zabensa a zaben 2019 dake tafe.

Kwamitin wanda aka kaddamar a jiya litinin, wannan Kwamiti shi ne babban kwamiti na koli na harkar takarar Malam Salihu Sagir Takai, wanda shi da kansa Malam Salihu Sagir Takai ne yake jagorantar kwamitin, a hada hadar zaben 2019 da za’a shiga nan gaba kadan.

Sanarwar nada wannan kwamiti ta fito ne daga hannu Barasta Faruk Iya Sambo, inda ya bayyana cewar, aikin wannan kwamiti ya ta’allaka akan yadda zasu jagoranci shirya yakin neman zaben Malam Salihu Sagir Takai, kuma, wannan shi ne babban kwamitin koli na yakin nman zaben.

Mambobin kwamatin sune, Dr. Bashir Galadanchi, Barrister Faruk Iya Sambo, Alhaji Ali Datti Yako, Hon. Ubale Jakada Kiru, Dr. Mahmoud Baffa Yola, Hon. Garba Shehu Fammar dakuma Hon. Idris Garba Unguwar Rimi.

Sauran su ne, Alhaji Kabiru Muhammad Tarauni, Hajiya Aishatu Mai-Jama’a, Comrade Munnir Matawalle, Hon. Sanusi Sani Barkum, Alhaji Lawal Tudunwada, Alhaji Tijjani Labaran Dambatta da kuma Alhaji Muktar Darki wanda zai kasance Sakataren wannan Kwamiti.

Sanarwar ta bayyana gamsuwa da jin dadin dukkan irin ayyukan da aka yi a kwamitin yakin neman zaben Malam Salihu Sagir Takai a 2011 da kuma 2015. Sannan kuma sanarwar ta kara da jinjina ga jagororin jam’iyyar PDP a jihar Kano, Ambasada Aminu Wali da kuma Malam Ibrahim Shekarau musamman irin gudunmawar da suka baiwa takarar Malam Salihu Sagir Takai.

LEAVE A REPLY