Ministar kudi, Kemi Adeosun

Daga Hassan Y.A. Malik

Masu hannun jari a kamfanin mai na Oando a karkashin kungiyar TSAN da PSA sun yi kira da a gaggauta tsige Ministar kudi ta Nijeriya, Kemi Adeosun a bisa zargin ta da suke yi da tsoma hannayenta a harkar hada-hada da canjin kudade.

Haka kuma sun zarge ta da da yin katsalandan cikin harkokin Hukumar Kula da Hannayen Jarin Manyan Kamfanoni.

Kungiyar ta yanke wannan hukunci ne bayan wani taro da ta zauna a jihar Lagos.

A wata sanarwa da suka fitar, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya tsige ministar, su na mai cewa ministar ta nuna kanta cewa ba ta son a yi bincike a badakalar Oando shi ya sa ta dakatar da tsohon shugaban SEC, Munir Gwarzo ta kuma cire darakta-janar na riko.

“Mun yi amanna da cewa cire minista Adeosun ne kadai zai tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa wannan gwamnatin da gaske ta ke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa a kowane bangare na tattalin arzikin kasar nan.”

LEAVE A REPLY