Daga Hassan Y.A. Malik

Kamfanin nan da ke kera motoci a Nijeriya, Innoson Motors zai dauki karin ma’aikata 3,000 da za su yi aiki a sabon reshen shi da ke jihar Anambara.

Kamfanin zai fara da daukan mutane 1,007 a wata mai kamawa na Afrilu, kafin daga bisani a dauki sauran.

Guraben da kamfanin ke son cikewa sun hada da Injiniyoyi, masu fenti, ma’aikatan sashen kudi, jami’an hulda da jama’a da sauran su.

Ga cikakken jerin guraben da za a cike da matakin karatun da ake bukata:

Welding Engineers- (SSCE, OND, HND, BSc)
Automotive Painters- (SSCE, OND, HND, BSc)
Plasterers- (SSCE, OND, HND, BSc)
Auto Electricians- (SSCE, OND, HND, BSc)
Mechanical Engineers- (SSCE, OND, HND, BSc)
Administration Officers-(HND, BSc)
Account Officers- (HND, BSc)
Public Relation Officers- (HND, BSc)
Marketing Executives (OND, HND, BSc)
Quality Control Officers- (HND, BSc)

Ga masu sha’awa, sai su tura takardun su wannan adireshin Email:
recruit@innosonvehicles.com kafin ranar Juma’ar, 6 ga watan Afrilun 2018.

LEAVE A REPLY