Rundunar tsaro ta kasa a Takum, dake jihar Taraba ta cafke wasu ‘yan kungiyar Sintiri su 9 sakamakon mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, an kama su ne da mallakar bindigar nan ta AK47.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar dake karkashin runduna ta 13, Kayode Owolabi ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya bayar da sanarwa ga manema labarai a ranar laraba a birnin Kalaba.

Su dai wadan da aka kama din, sun shiga hannu ne a kauyen Arufu dake tsakanin iyakar jihar Taraba da Bunuwai, rundunar soja karkashin bataliya ta 93 ce ta yi musu kofar rago.

“Rundunar sojan, karkashin bataliya ta 93 a ranar Litinin 8 ga watan Janarairu ta yiwa mutanan kofar rago, inda ta yi ram da su suna dauke da bindiga kirar AK47.

“Kafin a kai ga cafke mutanan dake karkashin kungiyar ‘yan Sintiri, sai da wasu mutane daga cikinsu suka yikokarin hana sojoji kama mutanan”

“A binciken farko farko da muka gudanar, mutanan sun ce makaman da suke aiki da su Gwamnatin jihar Bunuwai ce ta basu. Sun kuma tabbatar da cewar su kamar 60 a sansaninsu dake Pegie”

“Haka kuma, mutanana sun kuma tabbatar da cewar Gwamnatin jihar Bunuwai na biyansu 60,000 duk wata. Sannan sun kara da cewar kafin su fara yin aiki, sai da aka sanya tsaffin sjoji suka basu horo na musamman”

Mista Owolabi, ya ce, mutananda aka kama din yanzu suna baiwa jami’an tsaron sojan hadin kai, musamman wajen gudanar da binciken musabbabin faruwar wasu lamura.

Shugaban rundunar Ismaila Isa ya sha alwashin babu wani mai laifi da zasu bari ya tafi ba tare da an hukunta shi ba.

Sannan, ya godewa al’umma bisa yadda suke taimaka musu da bayanai wadan da suke kaiwa ga cafke masu laifi, sannan ya cigaba da cewar, rundunar sojan Najeriya zata cigaba da hada kai da al’umma domin cigaba da ayyukan tsaro a ko ina.

 

NAN

LEAVE A REPLY