Tsohon Shugaban kasa Cif Olushegun Obasanjo

Wani fitaccen dan jarida Mohamme Garba, ya kalubalanci tsohon Shugaban kasa Obasanjo kan ya fito ayi muhawara da shi a Talabijin kan wasikar da ya aikewa Shugaba Buhari inda yake bashi shawara kan kada ya tsaya zabe a 2019.

Mohammaed garba, wanda shi ne shugaban kamfanin Right Cantact Servises Ltd. ya bayyana hakan ne a Kaduna, inda ya kalubalanci wasikar ta Obasanjo, yace a zamanin demokaradiyya wannan wasika bata wuce shifcin gizo ba.

A cewarsa,babu wani dan Najeriya, duk girmansa da yake da ‘yancin hana wani mahaluki yin takara a kowanne irin mukami kuma ko waye shi, ‘yancin duk dan kasa ne ya fito ya tsaya zabe ko a zabe shi.

Daga nan, ya bukaci tsohon Shugaban kasa Obasanjo da ya bayyana dalilan da ya dogara a garesu daga kundin tsarin mulki da zai sanya ya hana wani mutum kamar Shugaba mai ci sayawa takara.

Mohammed garba yace zai dauki nauyin tattaunawar a duk gidan Talabijin din da Obasanjon ya zaba, daga nan sai ‘yan najeriya su yiwa Obasanjo tambayoyi kai tsaye na abinda yake nufi.

“Abu ne a bayyane cewar akwai matsin lamba daga kasashen waje, wadan da basa jin dadin yadda Shugaba Buhari ke tafiyar da al’amura a Najeriya, da ma wasu miyagun ‘yan Siyasa na cikin gida da basa yiwa najeriya fatan alheri”

“”Ina da fahimtar cewar wasu marasa kaunar Najeriya ne suke son yin amfani da Obasanjo domin kawowa zaben 2019 matsala, domin bakincikin arzikin da Allah ya huwacewa kasar”

“Ni Mohammed garba a matsayina na kwararren dan jarida, ina kalubalantar tsohon Shugaban kasa da ya fito muyi wannan muhawara kan wannan wasika da ya rubutawa Shugaba Buhari”

NAN

LEAVE A REPLY