A ranar Larabar nan ne aka kafa wata kungiya mai karfi ta Malaman addinin Musulunci ta Afurka. An kafa wannan kungiya ne a birnin Madina yayin da Malamai daga sassa daban daban na nahiyar Afurka suka hadu a kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Daga cikin Malaman da zasu wakilci Najeriya a wannan kungiyar akwai Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar Babban Limamin Masallacin Alfurqan dake Kano a matsayin mataimakin Shugaba mai lura da nahiyar Afurka ta yamma.

Sauran su ne, Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo a matsayin Shugaban kwamitin SHigo da sabbin mambobin kungiyar, sannan kuma Dr. Abdulmajid Abdulrazak Alaro shugaban kwamitin bincike da kuma fassara.

Ragowarsun hada da Dr. Khalid Abdulbaki Shugaban kwamitin watsa labarai da alakoki, sai kuma Sheikh Abdulwahab Abdallah Kano a matsayin Mamba a kwamitin wakafi tare da Dr. Abubakar Muhammad Sani Birnin-Kudu a matsayin mamba a kwamitin sulhu.

LEAVE A REPLY