Kabiru Tanimu Turaki SAN

Tsohon Minista a zamanin Gwamnatin Shugaban kasa Godluck Jonathan, kuma Shugaban kwamitin sulhu tsakanin Gwamnati da ‘yan Boko Haram a zamanin Gwamnatin PDP ta Jonatha, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki SAN, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Turaki ya bayyana wannan aniya tasa ne a gaban Shugabannin PDP na yankin shiyyar Arewa maso yamma da suka hada Masud Doguwa (PDP Kano) da Salisu Mamuda (PDP Jigawa) da Milgoma (PDP Sakkwatao) da Sanata Nasiha (PDP Zamfara) da Felix Hayat (PDP Kaduna) da Majigiri (PDP Katsina) da kuma Shugaban jam’iyyar PDP na ajihar Kebbi.

Anyi wannan taron ne a Kano, inda Kabiru Tanimu Turaki ya bayyanawa Shugaban jam’iyyara na shiyyar aniyarsa ta tsayawa takara tare da neman hadin kai da goyn bayansu.

Sanata Mas’ud Doguwa, wanda shi ne Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, ya tabbatar da mai neman tsayawa takarar cikakken goyon bayan jam’iyyar a jihar Kano, matukar shi ne dan takara, haka nan sauran Shugabannin jam’iyya na shiyyar suma sun tabbtar da hakan.

Kabiru Tanimu Turaki SAN, kwararren lauya ne, ya rike mukamin Minista zamanin Gwamnatin Jonathan, haka kuma, ya riki mukamin Shugaban kwamitin sulhu tsakanin Gwamnati da Boko Haram, bayan haka kuma, shi ne Shugaban kungiyar tsaffin Ministocin PDP a Najeriya.

 

LEAVE A REPLY