Mai baiwa Shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar wakilai ta kasa Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, kuma mai neman kujerar majalisar dattawa ta kudancin Kano ya koka akan yunkurin halaka shi da abokin takararsa Sanata Kabiru Gaya yake kokarin yi.

Kawu Sumaila ya bayyana hakan je a wata tattaunawa da yayi da manema labarai, inda ya bayyana cewar shi da kansa yaga mutanan da suke yunkurin halaka shi a lokacin da yake jawabi akan dandamali.

”Na hangosu kuma na tabbatar ba mutanan garin Sumaila bane, dan haka na sanya ‘Yan sanda suka kama su”

Kawu Sumaila ya bayyana cewar an samu mutanan da makamai bayan da aka kaisu wajen ‘Yan sanda a garin na Sumaila.

Sai dai Kawu ya dora alhakin wannan lamari akan Sanata Kabiru Gaya a yunkurinsa na ganin bayansa. Yabkara da cewar ya ankarar da jami’an tsaro akan yadda Kabiru Gaya yake yawo da ‘Yan daga da makamai.

LEAVE A REPLY