Tsohon Shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ya jinjinawa ‘yan majalisar kasa a sakamakon umarnin da suka bayar na sake sauya jadawalin zaben 2019, yace wannan sauyi zai taimaka wajen zabar mutane na gari a dukkan matakai.

Majalisar dattawa tare da takwararta ta wakilai, a wani taron manema labarai da suka yi sun amince da sake sauya jadawalin ranakun zaben 2019 mai zuwa.

A cewar ‘yan majalisun dokokin, zaben ‘yan majalisar tarayya shi ne zai zo farko, sannan ayi na Gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki na jiha, daga bisani kuma ayi na Shugaban kasa shi kadai.

Tsohon SHugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne, a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus a wata ziyarar girmamawa da ya kai masa babbar sakatariyar Gidauniyar Jonathan dake birnin Yenaguwa na jihar Bayelsa.

A cewar wata sanarwa da Ike Abonyi mai magana da yawun Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya fitar a babban taron kwamitin amintattun jam’iyyar PDP.

Sanarwar ta jiyo tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yana cewar, mutanen da suka dace ne kawai za’a dinga zaba in anyi haka, sannan kuma ya bukaci jam’iyyar APC mai mulki da ta kalli abin da idon basira.

“Daman can yin zaben Shugaban kasa a farko, yana tauyewa mutane masu mutunci damar samun nasararzabe, sabida bin yama da mutane suke yi albarkacin dan takarar Shugaban kasa”

” A sabida haka,jam’iyyar APC mai mulki, ya kamata ta kalli wannan batun sauyi da kyakkyawan nazari da fahimta, sannan kuma ta sani, ba anaa yin dokoki bane domin jin dadin mutanen da ke bisa mulki illa kawai sabida maslahar ‘yan kasa” A cewar Mista Jonathan.

 

LEAVE A REPLY