Kokawar Gargajiya a Jimhuriyar Nijar

A ranar litinn din nan ne aka fara Gasar cin Takobin kokawar gargajiya da aka saba gaudanarwa a Jimhuriyar Nijar. Wannan gasar dai ana yin ta ne a birnn Damagaran Zinder kuma karo na 39.

A yayin wannan kokawa wanda yayi Nasara zai lashe Takobi. Wanda ya lashe Takobin kuwa shi  ne Gwarzon Shekara na kokawa a Jimhuriyar Nijar.

Wannan gasar Kokawa na daya daga cikin muhimman wasannin gargajiya a Jimhuriyar Nijar. Domin mutanen da ke wajen Nijar kan koma gida a irin wannan lokacin domin kallon Kokawar,

‘Yan Nijar dai na baiwa wannan gasar Kokawa muhimmanci sosai, ta yadda mutane kan yi tafiya daga dukkan sassan Jimhuriyar Nijar domin shaida wannan wasan. Ana gudanar da wasan duk Shekara,inda ake samun wata jiha ta karbi bakuncin gasar.

LEAVE A REPLY