Marigayi Cif MKO Abiola

Jihohin Yarabawa da suka hada da Legas da Oyo da Ogun da Osun da Ondo sun ayyana ranar Talata 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu a daukacin jihohinsu domin tunawa da ranar da aka zabi Abiola a matsayin Shugaban kasa na farar hula kuma aka murde zaben.

Kwamishinan yada labarai da al’adu da yawon bude ido na jihar Oyo, Toye Arulogun shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai a madadin jihohin na Kudu maso yamma da aka ambata.

Ya kara da cewar zasu yi bikin cikar shekaru 25 da tunawa da ranarda aka zabi Abiola da Babagan Kingbe a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa a shekarar 1993, karkashin Gwamnatin IBB ta wancan lokacin, inda kuma daga bisani aka soke zabe.

Gwamnatin jihar Oyo tana alfahari da cewar zaben 12 ga watan Yuni, shi ne irin zabe na farko da aka gudanar a kasar nan da ba a taba yin zabe mai tsaftarsa ba, kasancewar babu inda aka ruwaito labarin ha’inci ko rashin gaskiya a yayin wannan zabe.

LEAVE A REPLY