Gwamnatin jihar Gombe aa Arewacin najeriya, ta bayyana cewar zata samar da audugar da ta kai hekta dubu goma a noman da za’a yi na wannan shekarar ta 2018, a kananan hukumomin 11 dake fadin jihar.

Shugaban hukumar cinikayya da fitar da amfanin gona, Musa Umar ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, a jihar Gombe a ranar Laraba.

Ya bayyana cewar, akwai shirin wata hadaka karkashin NIRSAL da zata samarda kudaden da za’a yi wannan noma.

“Muna son mu samarwa da manoman auduga kasuwa ta musamman, mu kuma samar musu da farashin da ya dace da kasuwar duniya”

Musa Umar yace zasu yi amfani da manoma 5,000 domin yin wannan muhimmin aiki, yayin da kowannen manomi zai noma hekta biyu ta auduga.

A cewarsa, a baya jihar Gombe itace tafi kowacce jiha samar da ingantacciyar auduga da ta dace da bukatar kasuwar duniya, amma yanzu abin ya sha bamban.

“Tuni muna da masaniya kan cewar, jihar Gombe itace jihar auduga a kasarnan a wancan lokacin, domin ana samar da audugar da ta kai tan 119,000 a shekara.

 

LEAVE A REPLY