Hassan Y.A. Malik

Wasu gimshikai a tafiyar jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun kammala shirye-shirye tsaf na sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP a daren yau Alhamis.

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Cif Olu Falae ne ya bayyana hakan, inda ya ke cewa, “Wasu tsofaffin gwamnoni kuma sanatoci masu ci a halin yanzu za su shiga jam’iyyar SDP a wani taro da jam’iyyar za ta gudanar a babban dakin taro na Ladi Kwali, Abuja, da misalin karfe 8:00 na dare.

Majiyar jaridar INDEPENDENT ta gano cewa, jiga-jigan sun zabi jam’iyyar SDP ne da nufin samar da jam’iyyar adawa ta uku da za ta ture APC da PDP daga mulkin Nijeriya.

LEAVE A REPLY